Gwamnatin Nijar, ta yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai a ranar 9 ga Satumba a birnin Doha, babban birnin ƙasar Qatar, wanda harin ya keta mutuncin Qatar a matsayinta na ƙasa.
A cewar gwamnatin Nijar, wannan ɗanyen aikin babban kutse ne ga dokokin ƙasa da ƙasa, Kundin tsarin Majalisar Dinkin Duniya da kuma ƙoƙarin samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.
Haka kuma gwamnatin Nijar ta yi kira da babbar murya ga ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa (musamman MDD) da ta tabbatar an yi hukunci a kan wannan ɗanyen aikin da Isra’ila ta aikata.
A ranar Talata, 9 ga Satumbar 2025, jiragen yaƙin Isra’ila suka kai hari kan manyan jami’an Hamas masu tattaunawar sulhu a birnin Doha na Qatar, inda aƙalla mutum biyar suka rasu.
