
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya mayarwa da shugabannin Faransa da Birtaniya da Canada, martani ka bukatar da suka yi na ya kawo ƙarshen hare-haren da sojijinsa suka sabuntawa a Gaza.
Shugabannin kasashen uku sun yi barazanar ɗaukan ƙwaƙwaran matakai muddin Isra’ila ta ci gaba da harin ta’addancinta a Falasdinu.
Shugaban na Isra’ila Netanyahu ya ce, waɗannan kalamai na ya dakatar da sabon hare-haren da cewa, u tamkar nuna goyon-baya ne ga kungiyar Hamas.
Tun a mokon jiya Isra’ila ta sabunta hare-haren da ta ke kai wa Gaza a wani wani sabon yunkuri na kawar da Falasdiwan daga yankin ta kargfin tuwo bayan ta hana kai musu daukin abincin da magunguna da haddas kiraye-kiraye daga Majalisar Dinkin Duniya na bala’in da ka iya biyo baya.
A ranar Litinnin ne Isra’ilan ta sassauta haramcin shigar da kayayyaki a Gaza, ga muhimman abubuwan bukatau kadai. Majalisar Ɗinkin Duniya na cewa hakan bai wadatar ba.