
Hukumar Bayar Da Agajin Gaggawa Ta Ƙasa (NEMA) reshen jihar Kano, ta sanar da karɓar ‘yan Najeriya 147 da aka dawo da su daga birnin Agadez ta Jamhuriyar Nijar.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X a ranar Litinin, ta bayyana cewa jirgin ‘yan gudun hijirar ya sauka a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da misalin ƙarfe 12:48 na rana, inda jami’an hukumar da sauran hukumomin da abin ya shafa suka tarbe su.
Daga cikin waɗanda aka dawo da su akwai maza 143, mace daya, da kuma yara ƙanana guda uku.
A cewar Hukumar Kula Da Ƙaura Ta Duniya (IOM), ta Majalisar Dinkin Duniya, dawo da ‘yan Najeriyar ya samu ne ta hanyar haɗin gwiwa da hukumomin da ke lura da harkokin ci-rani, da nufin dawo da su cikin koshin lafiya da mutunci.
NEMA ta kuma tabbatar da cewa an ba ɗaya daga cikin su kulawar gaggawa ta likita daga ƙungiyar agaji ta Red Cross, kasancewar yana fama da rashin lafiya.
Hukumar ta ce za a ci gaba da kula da waɗanda aka dawo da su, tare da taimakawa wajen gyara rayuwarsu domin su sake farawa cikin aminci.
Jamhuriyar Nijar ta ce ta yi hakan ne a wani ƙoƙari na ci gaba da rage wahalar da ‘yan ci-rani ke fuskanta a ƙasashen ketare.