
Babbar Kotun Tarayya dake Abuja, karkashin Mai Shari’a Idris Kutigi ta umurci Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio da ya bayyana a gabanta a ranar 9 ga Yuni 2025, domin amsa tuhumar bata suna da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ke yi masa.
Umurnin kotun ya biyo bayan bukatar da lauyan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, Barista Victor Giwa, ya gabatar, inda ya nemi a ba da izinin aika sammaci ga Akpabio ta hanyoyin da suka dace, bayan ya gaza halartar zaman kotu na 7 ga Mayu, 2025.
A cikin karar da aka shigar, Sanata Akpoti-Uduaghan ta zargi Akpabio da yin furuci ko kalaman da suka bata mata suna, wanda ta bayyana cewa sun yi mummunar illa a gare ta, illa da ta haifar da matsin lamba ga rayuwarta ta siyasa da ta sirri.
Saboda haka, ta nemi kotu ta tilasta masa biyan ta diyya mai tsoka da ta kai Naira biliyan 100.
Kotun, a yayin yanke hukuncin amincewa da bukatar masu kara, ta kuma umurci a kai sammacin ga Sanata Akpabio ta hannun magatakardar majalisar dattawa, tare da tabbatar da cewa an sanar da shi yadda ya kamata, kamar yadda doka ta tanada.
Majiyoyin shari’a da ke da kusanci da batun sun tabbatar da cewa sammacin ya riga ya isa hannun Sanata Akpabio bisa umarnin kotu.
A yanzu, idanu sun koma ranar 9 ga watan Yuni don ganin ko shugaban majalisar dattawan zai mutunta kotu ta hanyar bayyana a gaban ta domin kare kansa.