Ƙungiyar Ɗalibai ta Kasa (NANS) ta fara shirin wayar da kan ɗalibai domin gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar, don nuna rashin amincewa da sabuwar dokar haraji wacce ta fara aiki a ranar 1 ga Janairu, 2026.
Shugaban ƙungiyar, Olushola Oladoja, ya bayyana cewa ranar 14 ga Janairu, 2026, za ta kasance ranar ɗaukar mataki kan dokar a Najeriya.
A wata sanarwa, Oladoja ya nuna rashin dacewar aiwatar da dokar a ranar 1 ga watan Janairu, a daidai lokacin da ake yawaita kiraye-kiraye kan a dakatar da ita saboda zargin cushe.
Ya ƙara da cewa ƙaddamar da dokar haraji ba kawai abin takaici ba ne, har ma wani abu ne mai haɗari ga gwamnatin da ke ikrarin aiwatar da tsare-tsare na jama’a da bin ƙa’idodin dimokraɗiyya.
