
Ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa NANS, ta bai wa gwamnatin tarayya da ƙungiyar malaman jami’o’i ASUU, wa’adin kwanaki bakwai don su warware rikicin da ke tsakaninsu.
A wata sanarwa da ya fitar jiya Laraba, shugaban NANS, Olushola Oladoja, ya nuna damuwa kan yadda rikici ke ƙara ƙamari tsakanin gwamnati da ASUU, yana mai gargaɗin cewa ɗaliban kasar nan ba za su lamunci tsayawar karatu ba sakamakon yajin aiki.
Oladoja, ya ce an samu shekaru biyu ana karatu ba tare da yajin aiki ba a ƙarƙashin gwamnatin shugaba Bola Tinubu, sai dai sabon yajin aikin da ASUU ke yi yanzu na iya barazana ga wannan ci gaba.
Ya kuma nuna damuwa cewa jinkiri wajen aiwatar da yarjejeniyar da gwamnati ta yi da ASUU na ƙara haifar da rashin jituwa.
Ya roƙi Shugaba Tinubu, da ya sa baki kai-tsaye don kawo ƙarshen rikicin, yana mai gargaɗin cewa jinkiri wajen ɗaukar mataki na iya gurgunta ci gaban da aka samu a fannin ilimi.