
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Arc. Namadi Sambo, ya nuna gamsuwarsa da yadda Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ke gudanar da mulki musamman wajen cigaba da gyaran gine-ginen gwamnati da kuma saka dokar ta-baci a bangaren ilimi.
Namadi Sambo ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga Gwamna Abba da iyalan marigayi Alhaji Aminu Dantata, wanda rasuwarsa ta girgiza al’umma da dama a Najeriya.
A cewarsa, “Mutuwar Alhaji Aminu Dantata babban rashi ne ba kawai ga Kano ba, har da Najeriya baki ɗaya. Ya bar babban gibi a harkokin tattalin arziki da ci gaban al’umma.”
Sambo ya jinjina wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa irin jajircewarsa wajen sake farfado da gine-ginen gwamnati, musamman gidan gwamnati na Kano, tare da zartar da dokar ta-baci a fannin ilimi, matakin da ya ce zai taimaka wajen farfaɗo da ilimi a jihar.
Ya bukaci Gwamnan da ya ci gaba da gudanar da ayyukan alheri da ya fara, yana mai rokon Allah da ya kara masa lafiya da kwarin guiwa domin ci gaba da hidima ga al’umma.
A nasa jawabin, Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya gode wa Namadi Sambo bisa ziyarar da ya kawo domin yin ta’aziyya, yana mai bayyana marigayi Aminu Dantata a matsayin ginshiƙi a ci gaban tattalin arziki da ilimi a Najeriya da ma duniya baki ɗaya.
Gwamnan ya kuma yabawa irin gudunmawar da Namadi Sambo ya bayar a lokacin da yake Gwamnan Jihar Kaduna da kuma lokacin da yake mataimakin shugaban ƙasa.
Ya ce gwamnatin Kano za ta ci gaba da neman shawarwarinsa domin samun cigaba mai ɗorewa a jihar.