Hukumar Kididdiga ta Kasa, NBS, ta ce Najeriya ta samu riba ta kasuwanci ta naira tiriliyan 7.5 a Zangon na biyu na shekarar 2025.
Wannan ya nuna ƙaruwa da kashi 52 bisa 100 idan aka kwatanta da tiriliyan 5.17 da aka samu a zangon farko.
A cewar rahoton, jimillar cinikayyar kayayyaki ta ƙasa ta kai naira tiriliyan 38.037, wanda ya fi na zangon farko da kashi 5.5 bisa 100.
Hukumar ta ce shigo da kaya ya ragu zuwa tiriliyan 15.28 daga tiriliyan 15.42 na baya, abin da ya nuna saukar kashi 0.9 bisa 100.
Rahoton ya kuma nuna cewa fitar da kaya zuwa ƙasashen waje ya karu zuwa tiriliyan 22.75 daga tiriliyan 20.59 na baya, hauhawar kashi 10.49 bisa 100.
