Tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya ta aika saƙon gargaɗi ga sauran ƙasashen da ke fafatawa a gasar cin kofin nahiyar Afrika (AFCON), bayan ta doke Mozambique da ci 4–0 a wasan zagayen ‘yan ƙasashe 16.
Najeriya ta samu nasarar ne a wasan da aka buga ranar Litinin, inda ‘yan wasanta Ademola Lookman, Victor Osimhen da Adams Akor suka zura kwallaye, lamarin da ya tabbatar da ƙarfinta a gasar.
Da wannan sakamako, Najeriya ta tsallaka zuwa zagayen kwata fainal, inda za ta kara da wadda ta yi nasara tsakanin Algeria da Jamhuriyar Dimokuradiyar Congo.
Gasar cin kofin nahiyar Afrika dai na ci gaba da gudana a ƙasar Morocco, wadda ke karɓar bakuncin gasar.
