Gwamnatin Najeriya ta bayyana aniyar tattaunawa da gwamnatin Nijar domin warware rikicin diflomasiyyar da ke kunno kai tsakanin kasashen biyu.
Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, ya ce kasar na son ganin zaman lafiya da kwanciyar hankali a yammacin Afirka ta hanyar amfani da tattaunawa da diflomasiyya.
Ya ce gwamnati ta shirya tattaunawa tsakaninta da Nijar bisa ka’idojin ECOWAS saboda Najeriya tana mutunta ikon Nijar da iyakokinta tare da kira ga gwamnatin Nijar din da ta shiga tattaunawar domin neman mafita.
Tuggar ya gargadi duk wani yunkuri na yada zarge-zargen da ba su da tushe, yana mai cewa hakan ka iya haifar da rikice-rikicen da za su kawo cikas ga ci gaban Afrika.
Tuggar ya ja hankalin duniya kan rikicin, inda ya yi kira ga kasashen duniya da su tallafa wajen ganin an samu zaman lafiya a maimakon rura wutar rikici.
Ministan ya ce Najeriya ba za ta taba mara baya ga wani abu da zai kawo barazana ga tsaron Nijar ba.