
Ƙasar Saudiyya ta musanta rahotannin da ake yaɗawa na cewa ta sanya Najeriya a jerin ƙasashen da za ta hana biza.
A wata sanarwar da kasar ta fitar ta ce, daga ranar 13 ga Afrilu Saudiyya ba za ta bayar da biza ga ƙasashen Masar da Indiya da Pakistan da Morocco da Tunisia da Yemen da kuma Aljeria don ziyara da ko yawon buɗe ido ba.
Sanarwar ta kuma ce, rashin biyayya ga sabbin dokokin na iya janwo haramta wa kasashen shiga Saudiyya na tsawon shekaru biyar.
Sai dai, Cibiyar Yawon Buɗe Ido ta Saudiyya ta bayyana wa manema labarai cewa waɗannan sabbin dokoki na takaitaccen lokaci ne wanda ya shafi lokacin aikin Hajji kadai.
Sanarwar ta kuma ci gaba da cewa, duk wanda ke da biza ta ziyara ba zai iya yin aikin Hajji ko zama a birnin Makka daga ranar 10 zuwa 14 ga Thul Qida ba.
Bizar aikin Hajji za ta kasance kawai a lokacin aikin Hajji.
Hukumar ta tabbatar da cewa duk wani dan Saudiyya da ya cika sharuɗɗan zai iya yin Hajji kamar yadda aka saba.