
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC, na cigaba da sa ido akan wasu jerin magungunan da sauran wasu kayayyaki da ake amfani da su da hukumar ta soke lasisinsu.
Hakan ya biyo bayan daina bayar da izinin shigo dasu da rarraba su, ku ko kuma sayar dasu a fadin kasar.
A kwanakin nan ne Hukumar NAFDAC ta bayyana sunan wasu magunguna 101 da abun ya shafa a shafinta na Intanet.
Darakta mai kula da inganci da tantance magungunan da ake sayarwa a kasuwanni a hukumar ta NAFDAC, Bitrus Fridon, ya bayyana dalilan daya sanya hukumar janye lasisin magungunan
To ko wadanne magunguna hukumar ta NAFDAC ta janyewa lasisi, ga abun da Bitrus Fridon ke cewa…
Jami’in hukumar ta NAFDAC, yayi kira ga al’umma da su dinga sanar da hukumar duk wani abinci ko maganin da basu yadda da ingancinsa ba ga ofisoshin hukumar, domin daukar matakin da ya dace.