Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ta kori dalibai 60 daga sassa daban-daban na Jami’ar bisa zargin satar amsa a lokacin jarabawa.
Jami’ar ta yanke wannan hukunci ne yayin taron hukumar gudanarwa karo na 43 da aka yi a ranar 7 ga Janairu, 2026, bayan nazari kan rahotanni da shawarwarin da hukumomin ilimi da na ladabtarwa suka gabatar.
An bayyana wannan mataki ne ta cikin wata sanarwa da hukumar jami’ar ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Juma’a.
A cewar sanarwar, bincike ya nuna cewa daliban da abin ya shafa sun aikata wasu laifuka da suka saba wa dokokin jarabawa na jami’ar.
