Kungiyar kwallon kafa ta Leicester City ta raba gari da kocinta Ruud van Nistelrooy, kimanin mako shida bayan ƙungiyar ta faɗa rukuni na biyu na gasar Ingila.
Mai shekara 48 ya jagoranci ƙungiyar a wasa guda 27, inda a ciki suka yi rashin nasara 19, sai nasara a wasa biyar a duka wasannin kakar da ta gabata.
Leicester ta yi ban-kwana da Premier League ne tun ana sauran wasa biyar a kammala gasar, amma duk da haka ƙungiyar ta bar tsohon ɗanwasan gaban na Man United ya kai har ƙarshen kakar.
Ƙungiyar ta ce ta rabu da Van Nistelrooy ne bayan tattaunawa ta fahimtar juna, domin fara shirin fuskantar abin da ke gabansu.
Sai dai ƙungiyar na fuskantar ƙalubale babba, kasancewar duk da cewa ta faɗa ƙaramar gasar, yanzu haka tana fuskantar ƙalubalen cire maki a kaka mai zuwa bayan hukumar ƙwallon ƙafar Ingila ta zarge ta saɓa dokokinta a kakar bara.
