Sanarwar korar ministan Abuja Nyseom Wike daga jamiyyar PDP ta bar baya da kura, bayan da wasu daga cikin gwamnonin jamiyyar suka fara barranta kan su da waccan sanarwa, na baya bayan nan shine Gwamna Caleb Mutfwang na Jihar Filato wanda ya bayyana cewa bai da hannu ko alaka da korar Wike, daga jam’iyyar PDP.
- Zargin kisan kiristoci: Aikin jam’iyyun hamayya da Ƙasashen Waje ne – Wike
- 2027: Wike ya magantu game da takarar Jonathan da Turaki a PDP
Tun da farko an rawaito gwamnan Adamawa Ahmadu Fintiri na cewa sam babu yawunsa a korar Wike daga Jam’iyyar
A Asabar din nan ne dai anarwa ta gabata cewa Jamiyyar a wurin babban taron ta da take gudnarwa yanzu haka a birnin Badun na jihar Oyo ta yanke shawarar korar Nyesom Wike, da Sanata Samuel Anyanwu da kuma tsohon Gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose, daga jam’iyyar bayan an zrge u da cin amanarta da yi mata zagon kasa
