Ƙungiyar Kare Haƙƙin Bil’adama ta Ƙasar Kenya ta bayyana cewa aƙalla mutane 16 ne suka rasa rayukansu yayin da sama da 400 suka jikkata a wata gagarumar zanga-zangar adawa da dokar haraji da aka gudanar a babban birnin Nairobi da wasu manyan birane a ƙasar.
Dubban matasa da sauran jama’a sun fito titi suna rera waƙoƙin “Ruto dole ya sauka,” suna ɗaga tutoci da allunan da ke nuna fushinsu da yadda ake tafiyar da mulki da kuma ƙarin haraji da gwamnati ke shirin aiwatarwa.
Ƴan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye, ruwan zafi da harsashi wajen tarwatsa masu zanga-zanga, lamarin da ya janyo asarar rayuka da jikkata da dama.
Kungiyoyin kare haƙƙin bil’adama da dama, ciki har da Amnesty Kenya, sun zargi jami’an tsaro da amfani da karfin tsiya.
Gwamnati ta ƙoƙarta hana gidajen rediyo da talabijin ɗaukar zanga-zangar kai tsaye, amma babbar kotu a Nairobi ta dakatar da wannan ƙuduri, tana mai cewa hakan cin fuskar ‘yancin faɗar albarkacin baki ne.
Shugaba William Ruto ya yi kira ga masu zanga-zangar da su zauna lafiya, yana mai cewa yana da muhimmanci a guji duk wani abu da zai kawo rikici.
Amma duk da haka, wasu daga cikin masu zanga-zangar sun ƙuduri aniyar kai farmaki gidan shugaban ƙasa, wanda ƴan sanda suka dakile.
