
Hadarin zabatarewar kasa da ya faru a Saliyo a 2017 da hallaka rayuka
Hukumomi a kudancin Ghana na ci gaba da aikin ceto bayan wata mahaƙar ma’adinai da ta rufta, inda ake fargabar cewa akalla mutum 30 sun makale a ƙarƙashin ƙasa tun ranar Laraba.
Har yanzu dai babu cikakken bayani kan musabbabin hatsarin da ya afku a ƙauyen Akyem Wenchi, da ke gundumar Denkyembour a yankin gabashin kasar.
An tabbatar da mutuwar mutane uku a lamarin, yayin da wani mutum guda ke kwance a asibiti cikin mawuyacin hali.
A halin yanzu dai jami’an ceto na kokarin kai dauki, duk da ƙalubalen da suke fuskanta a wurin da lamarin ya faru.
Shugaban yankin kuma shugaban majalisar tsaron yankin, Umar Ahmed, ya bayyana cewa aikin ceto ya fuskanci cikas sakamakon tarin fusatattun matasa da mazauna yankin da suka mamaye wajen.
Ya ce hayaniyar jama’a da rashin tsaro sun tilasta jami’an tsaro da masu aikin ceto ficewa daga yankin.
“Mun ji kamar muna cikin barazana,” in ji Umar Ahmed ga kafafen yaɗa labarai na ƙasar. “Lokacin da matasan suka iso suna rera waƙoƙi da nuna fushi, dole muka bar wajen don kare rayukan ma’aikata.”
Ruftawar wannan mahaƙa na ƙara haskaka matsalar haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a yankin, inda jami’an tsaro a Akwatia ke jima suna fafutuka da masu wannan haramtacciyar sana’a.