Gwamnatin Jihar Gombe ta tabbatar da bullar zazzabin Lassa a jihar, inda aka tabbatar da mutum 11 sun kamu da cutar, yayin da mutum ɗaya ya rasu.
Kwamishinan Lafiya na Jihar Gombe, Dakta Habu Dahiru, ne ya bayyana hakan a yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka mayar da hankali kan shirin tinkarar barkewar cututtuka a jihar.
Dakta Dahiru ya ce marigayin ya fara nuna alamun zazzabin Lassa ne a Jihar Taraba, kafin daga bisani a mayar da shi Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Gombe domin samun kulawar lafiya, inda ya rasu.
Ya bayyana cewa yawancin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar na daga cikin mutanen da ke yawan zuwa Jihar Taraba domin gudanar da ayyukan noma.
Kwamishinan ya tabbatar da cewa Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Gombe na ci gaba da aiki kafada da kafada da Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaduwa ta Ƙasa (NCDC), Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), da kuma UNICEF domin dakile yaduwar cutar.
Dakta Habu Dahiru ya jaddada ƙudirin gwamnatin jihar na haɗa kai da gwamnatocin jihohin Adamawa, Taraba, Bauchi da Plateau domin hana yaduwar cutar baki dayan ta.
