Hukumar Shirin Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya WFP ya yi gargadin cewa aƙalla mutane miliyan 35 a arewacin Najeriya na iya fuskantar matsanancin rashin abinci a shekara mai zuwa.
Wannan gargadin ya biyo bayan ƙaruwar hare-haren ‘yan bindiga da kuma tabarbarewar tsaro a yankin.
Wani mai magana da yawun hukumar ya bayyana cewa al’ummomi da dama na fama da matsaloli sakamakon karuwar hare-haren ‘yan bindiga da kuma yanayin tattalin arzikin ƙasar, wanda ya sa bukatar tallafi ta karu.
Ayyukan tallafin abinci na hukumar, waɗanda ke samar da abinci mai gina jiki a arewa maso gabashin Najeriya, sun sha jinkiri a ‘yan watannin da suka gabata.
Haka kuma, an bayyana cewa abincin tallafi da ake da shi yanzu zai ƙare nan da watan Disamba, abin da ke nuna gaggawar samar da tallafi don gujewa bala’in jin kai.
