Ministan Harkokin cikin gida na ƙasar Kenya Kipchumba Murkomen yace akalla mutane 21 sun mutu, wasu 31 kuma sun ɓace a yammacin kasar Kenya bayan zaftarewar ƙasa da ruwan sama mai ƙarfi ya haifar.
Ministan ya yi kira ga mutanen da ke zaune kusa da kogunan da yankunan da zaftarewar ƙasa ta shafa da su koma wurare mafi aminci.
Baya ga mutuwar mutane 21 da 30 da suka ɓace, Ministan ya ba da rahoton cewa an kai mutane 25 da suka ji rauni zuwa garin Eldoret da ke yammacin Kenya.
Hukumar agajin gaggawa ta ƙasar ta fitar da hotunan sama na yankin da ke nuna irin barnar da aka fuskanta a yankin.
Sanarwa daga hukumar na nuni da cewa ta na aiki da nufin kokarin zakulo mutanen da suka bata tare da goyon bayan gwamnati, gami da ɗaukar waɗanda suka ji rauni ta jirgin sama.
