Da safiyar Juma’a, 13 ga watan Fabrairun 1976, aka yiwa Shugaban mulkin soja na Najeriya, Janar Murtala Ramat Muhammed, kwanton-ɓauna sannan aka kashe shi a wani juyin mulkin da bai yi nasara ba. #murtala
Mulkinsa na ɗan gajeren lokaci ne, amma ya zama wani mizani na gaskiya da kishin ƙasa da kuma cigaba mai dorewa.
Bayan ya kwaci mulki daga Janar Yakubu Gowon a watan Yulin 1975, Murtala ya fara kawo sauye-sauye ba tare da bata lokaci ba.
Shugaban na mulkin soja ya ƙaddamar da yaƙi da rashin ɗa’a, a inda ya kori dubban ma’aikatan gwamnati da aka zarga da rashawa da kuma cin hanci.
Ya kuma goyi bayan samun ’yancin Afirka, kuma ya fara aikin sauya babban birnin Najeriya daga Legas zuwa tsakiyar Najeriya watau Abuja.
Murtala ya kuma ƙirƙiri sabbin jihohin Bauchi da Binuwai da Borno da Imo da Neja da Ogun da Ondo. Hakan ya ƙara yawan jihohin Najeriya daga 12 zuwa 19.
Wannan mataki ya kasance ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ake ci gaba da tuna mulkinsa na gajeren lokaci.
Kisan da aka yi masa ya katse wannan shirin sauya tsarin da har yanzu ake ganin babu wanda ya kai shi.
An haife Murtala a unguwar Kurawa a birnin Kano, a ranar 8 ga watan Nuwamba 1938. Ya yi karatunsa a Kwalejin Barewa, sannan ya halarci makarantar sojoji ta Royal Military Academy da ke Sandhurst a Ingila.
La’akari da wadannan ta sa aka sa hotonsa a takardar Naira 20 da kuma sunansa a manyan gine-gine a Najeriya ciki har da filin jirgin saman Legas da makarantu da tituna da asibitoci a fadin kasar.
