Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta ce tana ci gaba da tuntuba kan jadawalin babban zaɓen 2027, bayan da aka nuna damuwa cewa ranar zaɓen ta yi daidai da watan Ramadan.
A wata sanarwa da Kwamishinan Ƙasa kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Masu Zaɓe, Mohammed Haruna, ya fitar, hukumar ta ce an tsara ranakun ne bisa tanadin Kundin Tsarin Mulki na 1999 da dokar zaɓe ta 2022 da kuma ƙa’idojin INEC.
INEC ta sanya 20 ga Fabrairu, 2027 domin zaɓen Shugaban Ƙasa da na Majalisar Dokoki ta Ƙasa, yayin da zaɓen gwamnoni da na majalisun dokokin jihohi zai gudana a 6 ga Maris, 2027.
Sai dai wasu ‘yan Najeriya, ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, sun buƙaci a sake duba ranakun, suna mai cewa sun faɗa cikin watan azumi, wanda ka iya shafar yawan fitowar masu zaɓe.
Haruna ya ce hukumar na duba lamarin, kuma idan buƙatar hakan ta taso, za ta nemi matakin Majalisa domin tabbatar da gudanar da zaɓe mai haɗa kowa
