
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya ce, gwamnatin ta samu nasarar rage hare-haren ta’addanci da na ‘yan bindiga.
Rabadu ya kuma ce, lokaci ya yi da ‘yan bindiga da ke addabar Arewacin Najeriya su zo su miƙa wuya.
Babban Jami’in tsaron bayyana hakna ne a hirarsa da BBC a ranar Talata.
“Ana kai wa hari a gidajen yari da jirgin ƙasa da sansanonin sojoji, amma yanzu an daƙile hakan tun bayan da wannan gwamnati ta hau mulki”. In ji shi.
Sannan ya kuma ce, gwamnatinsu ta hallaka shugabannin ‘yan bindiga kimanin 300.
Bayanansa na zuwa ne mako guda makon bayan ‘yan bindiga sun kashe mutane a Kauran Namoda a Jihar Zamfara.
Sannan ƙungiyar Boko Haram har yanzu na ci gaba da zama barazana a Arewa Maso Gabas.