
Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa yanzu ana iya yin tafiya a hanyar Abuja-Kaduna da dare ba tare da fargabar hari daga ’yan ta’adda ba, sakamakon matakan tsaro da gwamnati ta ɗauka.
Ribadu ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin wani taron tattaunawa tsakanin gwamnati da al’umma wanda Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello ta shirya a Kaduna.
Ya ce jami’an tsaro sun samu nasarar fatattakar ’yan ta’adda da suka dade suna addabar hanyar, lamarin da ya haifar da dawowar zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Ya kara da cewa tuni jami’an tsaro suka dakile yunkurin kai hare-hare da dama da ’yan ta’adda suka yi kan jirgin ƙasa da ke tsakanin Abuja da Kaduna, wanda ya kasance cikin barazana tun bayan harin da aka kai a shekarun baya.