
Sanata wakiltar mazabar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa Ali Ndume ya soki nadin mukamai da Shugaba Bola Tinubu ke yi, yana mai cewa hakan ya ci karo da tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya.
Sanatan ya fadi hakan ne a hirarsa da gidan talabijin na Arise a farkon makon nan, Sanatan ya bayyana cewa yadda ake raba mukaman siyasa a yanzu bai dace da sashi na 14(3) na tsarin mulkin 1999 da aka yiwa gyara ba.
Sanatan ya kara da cewa tsarin mulkin Najeriya na bukatar a bai wa kowane yanki wakilci cikin gwamnati, yana mai jaddada cewa ba yana nufin shugaban kasa ba zai iya yin nade-naden da ya dace ba, amma dole ne ya bi doka.
Ndume ya yi nuni da cewa a dinga duba nade-naden da idon doka, domin idan aka ci gaba da watsi da tsarin da kundin tsarin mulki ya shimfida, hakan na iya haifar da matsala a nan gaba.