
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya jaddada mubayi ‘arsa da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso kuma jagoran kwankwasiya.
Gwaman ya fadi hakan ne a jawabinsa a wajen bikin cikar Kwankwaso shekaru 69 da haihuwa da aka gudana a Gidan Kwankwasiyya dake titin Miler Road a jihar Kano ranar Talata.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma yi addu’a ga duk mai son ya ga rabuwarsu da Kwankwaso da ya ji kunya.
“Duk munafukai na gida da na waje da ke son su ga mun rabu da Kwankwaso to ku gaya musu karyar su ta sha ƙarya.
“Da Kwankwaso, da Abba da yan jam’iyya duk muna nan daram-dam…. Allah kai mana maganin wadanda basa son zaman lafiyarmu”. In ji shi.
Gwamnan ya kuma yi addu’ar Allah Ya yi maganin waɗanda ya kira da munafukai dake son haddasa rikicin tsakaninsa da mai gidan nasa.
Ya kuma kamata duk mai kushe shi kushe shi, ba mai son ci gaban al’umma ba ne.