Dan majalisa mai wakiltar Doguwa da Tudun Wada daga jihar Kano, Alhassan Ado Doguwa, ya yi kakkausar suka ga gwamnatin tarayya da ita majalisar kanta, akan matsalar taaddanci da ta addabi kasar nan.
A muhawarar da aka tafka, a wani zama na musamman da majalisar wakilai ta gudanar a jiya Talata, Doguwa ya zargi gwamnatin tarayya da gazawa dalilin da yasa ya bukaci a rufe Majalisar da dakatar da ayyukanta na yau da kullum har sai an samar da mafita.
Doguwa ya kuma nemi a ayyana dokar ta-baci domin bai wa batun tsaro muhimmancin da ya kamata.
Ya bayyana cewa lamuran tsaro sun kai wani mataki mai tayar da hankali yana cewa al’ummar da suke wakilta suna cikin mawuyacin hali na rashin kwanciyar hankali musamman a Arewa inda manoma ba sa iya zuwa gonaki, yan kasuwa kuma ba sa iya zuwa cin kasuwa saboda hare haren da yan ta’adda ke kaiwa baji ba gani.
Ya nemi goyon bayan shugaban majalisar wakilai, Tajuddeen Abbas, da sauran mambobi domin tursasa gwamnati ta dauki matakin gaggawa wajen kare rayuka da dukiyoyin ƴan kasa.
