Mazauna karamar hukumar Bagwai da Shanono sun bukaci duk wanda ya samu nasara a zaben cike gurbin dan majalisa mai wakiltan su a zauren majalisar dokokin Kano, da ya fifita bukatun al’ummar yankin musamman bangare ababan more rayuwa.
Ana dai gudanar da zaben cike gurbin ne bayan da Allah ya karbi ran tsohon Dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin biyu Halilu Kundila.
Wakilan mu Kamal Umar Kurna da Ammar wakili Shanono da suka halarci rumfunan zaben, sun rawaito cewar tun da misalin karfe 8 na safiya aka fara gudanar da zaben wanda yake cike da tsattsauran tsaro daga jami’an ‘yan sanda ta takwarorin su.
Wasu daga cikin wadanda suka kada kuri’un su kuma wakilan namu suka zanta dasu sun bayyana gamsuwa da yadda zaben yake gudana.
Wakilan namu sun rawaito cewa, abinda suka lura dashi shine yadda na’urar tantamce masu kada kuri’ar take kawo tsaiko wajen gudanar da zaben.
