Sabbin alkaluman (CPI), 2024 sun nuna cewa Najeriya ta matsa daga matsayi na 145 zuwa 140 cikin ƙasashe 180 mafi cin hanci a duniya.
Duk da wannan sauyi, Najeriya na ci gaba da zama ɗaya daga cikin ƙasashen da cin hanci ke yawaita, sakamakon gazawar mahukunta wajen tafiyar da mulki a fayyace.
CPI na tantance cin hanci a ƙasashe ta hanyar bayar da maki daga 0 zuwa 100—inda mafi ƙarancin maki ke nuna cin hanci mafi muni, yayin da mafi girma ke nuna shugabanci nagari.
A wata sanarwa da ta wallafa a X a safiyar yau Talata, shugabar Transparency International, François Valérian, ta bayyana cin hanci a matsayin babbar barazana ga duniya.
Najeriya ta kasance a matsayi na 146 da maki 26 a 2019, ta koma 154 a 2021 da maki 24, sannan 145 a 2023 da maki 25.
