
Gwamnan Neja Umar Mohammed Bago, ya saka dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 12 a Minna babban birnin Jihar.
Ya kuma umarci jami’an tsaro su kama ƴandaba da duk waɗanda ke da hannu wajen tayar da zaune tsaye a Minna, babban birnin jihar.
“An haramta zirga-zirgar baburan ’yan acaɓa da masu Keke Napep daga ƙarfe 6 na yamma zuwa 6 na safe, a rika cafke matasa masu gashin dada tare da masu yin askin da bai kamata ba….” in ji shi.

Mai taimakawa gwaman jihar a kan siyasa da tsare-tsare, Mohammed Nma Kolo ya ce, sai da gwamna ya zauna da masu ruwa da tsaki kafin daukar matakin…
Ya kuma ce, jama’ar jihar sun sha wahala a ‘yan kwanakin nan, saboda haka daukar matakan ya zama wajibi domin kare rayuka.
Rahotanni daga Minna sun bayyana cewa jama’a sun goyi bayan matakan da gwamnan ya dauka domin magance matsalar tsaro a jihar.
A hirar premier radio da wani dan Jarida Sulaiman Ibrahim a jihar ya ce, daukar matakin ya biyo bayan yawaitar hare-hare da kashe-kashe ne a birnin.
Ya kuma kara da cewa, tun a cikin watan azumin da ya aka fara samun tsanantar ayyukan rashin tsaro a jihar…
Sulaiman Ibrahim ya shaida mana cewa jama’ar garin na fatan matakan za su taimaka wajen dawo da zaman lafiya zuwa jihar.