
Wasu gungun matasa sun gudanar da zanga-zangar lumana a garin Yola ta Jihar Adamawa, don jan hankalin gwamnati kan ƙaruwar talauci da yunwa.
Masu zanga-zangar sun rufe manyan tituna, inda suka din ga kira ga Gwamnatin Tarayya da ta jihar, da su ɗauki matakan rage wahala, rashin aikin yi da matsalar tsaro da ta addabi ƙasar nan.
Shugaban Ƙungiyar MOTION na Jihar Adamawa, Mista Musa Andrew da ya jagoranci zanga-zangar, ya ce zanga zangar ta zama dole saboda halin matsin tattalin arziƙi da ke ƙara taɓarɓarewa.
Ya kuma bayyana damuwa kan matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara musamman a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.