Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wasu matasa biyu bayan da suka fada cikin wani tafkin a yankin Ring Road Kureken Sani da ke karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano.
Sanarwar da Kakakin hukumar Saminu Yusif Abdullahi ya fitar, tace matasan biyu masu shekaru 18, Sadiq Isyaku da Auwal Isyaku, sun fada cikin wani tafkin a ranar litinin
Rahoton farko ya nuna cewa matasan na kokarin tserewa ne daga wasu da ake zargin ’yan kwacen waya ne da ke binsu, inda a kokarinsu na tsira suka fada cikin tafkin.
An ciro su daga ruwan a sume, amma daga bisani aka tabbatar da rasuwarsu. Daga nan aka mika gawarwakinsu ga mahaifinsu Ibrahim Shehu da ke zaune a Unguwa Uku a Kano.
A wani lamari dabam, hukumar kashe gobarar ta ce ta ceto wani mutum mai kimanin shekaru 40, bayan da ya fada cikin wata rijiya a Durumin Zungura kusa da Assahabul Khahafi a karamar hukumar Birni.
Hukumar ta ce ta samu kiran gaggawa daga Abdullahi Aminu da misalin karfe 7:12 na dare ranar Litinin, 9 ga Maris, 2026, wanda ya sanar da cewa wani mutum ya fada cikin rijiya.
Jami’an ceto daga hedikwatar hukumar sun isa wurin da gaggawa, inda suka gano mutumin mai suna Shitu Balarabe a cikin rijiyar. Daga bisani sun samu nasarar ciro shi da rai.
An mika shi ga dan’uwansa Jamilu Balarabe da ke zaune a Durumin Zungura a cikin birnin Kano.
Hukumar kashe gobarar ta jajantawa iyalan wadanda suka rasu tare da kira ga jama’a da su dauki matakan kariya domin kauce wa irin wadannan hadurra.
