
Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP na Arewa sun amince da tsohon Ministan Ayyuka Na Musamman Da Harkokin Gwamnati, Kabiru Tanimu Turaki, SAN, a matsayin dan takarar da suka amince da shi ya zama shugaban jam’iyyar na kasa.
Hakan na zuwa ne gabanin babban taron jam’iyyar na kasa da za a gudanar a birnin Ibadan na jihar Oyo a shekarar 2025.
An cimma wannan matsayar ne bayan wani gagarumin taron tuntuba da masu ruwa da tsak n jam’iyyar na Arewacin kasa suka gudanar a Abuja.
A cewar majiyoyi a wurin taron, amincewar na da nufin gabatar da matsayar Arewa guda daya gabanin babban taron da aka shirya gudanarwa daga ranar 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba, 2025.