Manoma kimanin 2,143 a Jihar Kaduna sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta tallafa musu da kayan aikin noma kyauta ko a farashi mai sauƙi.
Manoman sun ce sun yi asarar sama da naira biliyan 10 a kakar noman bara, sakamakon faɗuwar farashin masara da tsadar kayan noma.
Sun koka da hauhawar farashin taki, inda buhun NPK ke kai naira 60,000, yayin da Urea ta kai naira 50,000.
Manoman sun gargaɗi cewa idan ba a kawo musu ɗauki ba, da dama daga cikinsu ba za su iya yin noma a kakar bana ba, musamman a Arewa.
Sun buƙaci Babban Bankin Nijeriya ya rage farashin kayan noma domin ƙara samar da wadataccen abinci da bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.
