Kungiyar Manchester City ta sha kasha a hannun Manchester United a wasan mako na 16 a Premier League ranar Lahadi a Emirates.
Manchester United ya doke Manchester Citya da ci 2 da 1.
City ce ta fara cin ƙwallo tun kafin hutun rabin lokaci. Sauran minti biyu a tashi daga wasan United ta farke ta hannun Bruno Fernandes. Sannan Ahmad Diallo ya kara na biyu daf da za a tashi daga karawar.
Man City ta yi nasara ɗaya tal daga karawa 11, yayin da aka doke ta sau takwas sannan ta yi canjaras sau biyu.
Maki 27 da Man City da take da shi bayan wasannin mako na 16, kuma wannan shi ne rashin kokari da kungiyar ta yi tun 2010.
A tarihin gasar dai Manchester United ce kaɗai da maki 27 bayan mako na 15 ta je ta lashe Premier League a kakar 2002/03.