Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya musanta jita-jitar da ke yawo cewa yana shirin ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Makinde ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi a bikin ƙaddamar da wani littafi da tsohon Ministan Yaɗa Labarai na Ƙasa, Lai Mohammed, ya wallafa.
Ya jaddada cewa har yanzu yana nan daram a cikin jam’iyyar PDP, duk da cewa wasu gwamnonin jam’iyyar sun sauya sheƙa zuwa APC a baya-bayan nan.
Gwamnan ya kuma bayyana damuwa kan yadda wasu ’yan siyasa ke amfani da addini, ƙabilanci da bambancin yanki wajen rarraba al’umma domin cimma muradunsu na siyasa.
A cewarsa, mafi yawan ’yan Najeriya na son zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasa, amma ayyukan wasu ’yan siyasa na haddasa rarrabuwar kawuna a cikin al’umma.
Makinde ya yi kira ga shugabanni da su haɗa kai, ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba, domin inganta shugabanci mai kyau da tabbatar da ci gaban Najeriya.
