Gwamnan Jihar Oyo kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Allied Peoples Movement, APM, Seyi Makinde, ya bayyana cewa jam’iyyun adawa na tattauna yiwuwar cimma yarjejeniyar haɗin kai domin fafatawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.
Makinde ya bayyana cewa haɗin kan zai iya kasancewa tsakanin jam’iyyu da ‘yan takarar shugaban ƙasa masu ra’ayin kawo sauyi a shugabancin Najeriya.
Tun da farko, gwamnan ya tabbatar da gudanar da tattaunawa da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, da kuma tsohon Gwamnan Anambra, Peter Obi, kan yiwuwar haɗin gwiwar siyasa.
Ya ce sakamakon tattaunawar zai iya sa su yi aiki tare ko kuma su ci gaba da fafatawa da juna a zaɓen.
Makinde ya bayyana cewa duk wata matsaya kan haɗin kan za ta dogara ne da nazarin bayanai, ra’ayoyin jama’a da kuma abin da ɓangarorin suka amince da shi.
A baya, jam’iyyun adawa shida, ciki har da ADC, APM, NDC, SDP, PDP da PRP, sun gudanar da shawarwari domin lalubo hanyoyin haɗin kai gabanin zaɓen 2027.
Sai dai har yanzu ba a tabbatar da wata yarjejeniya ta ƙarshe da ta haɗa dukkan ‘yan takarar adawar ƙarƙashin ɗan takara guda ba.
