Majalisar dokokin jihar Nasarawa, ta yiwa kasafin kudin shekarar 2025 da aka amince da shi a baya gyara daga Naira biliyan 402.5 zuwa Naira biliyan 384.3.
Shugaban majalisar, Danladi Jatau, ne ya sanar da amincewa da gyaran kasafin kudin da aka yiwa kwaskwarima a zaman gaggawa da majalisar tayi.
Majalisar ta bayyana cewa ta rage yawan kudin daga Naira biliyan 402.5 zuwa Naira biliyan 384.3
Hakan ya biyo bayan shawarar da Hukumar Zartaswar jihar ta bayar na cewa kasafin kudin da aka amince da shi a baya zai zarce kudaden shigar da jihar ake hasashen zata samu a shekarar 2025.
Tun da farko, shugaban masu rinjaye na majalisar, Suleiman Azara, shine ya gabatar da kudirin dokar wadda ta tsallake karatu na uku, yayin da shugaban marasa rinjaye, Luka Zhekaba, ya amince da kudirin.