Majalisar dokokin kano ta fara yinkurin samar da wata doka wadda zata tilasta yin amfani da harshen uwa musamman yaren Hausa a matsayin hanyar koyarwa a makarantun jihar, domin bunkasa fannin ilimi.
Hakan ya biyo bayan kudurin da Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Takai a zauren Dr Musa Ali Kachako ya gabatar.
Da yake karin bayani a gaban majakisar, Dr Kachako yace samar da dokar zai dace da yadda tsarin koyarwa yake a duniya kamar yadda kasashen da suka ci gaba irin su China, Japan da India suka samu babbar nasara ta hanyar yin amfani da harshen uwa wajen koyarwa a makarantun su.
Dr Kachako ya kara da cewa rungumar harshen uwa a matsayin hanyar koyar da dalibai zai karawa dalibai fahimta da san karatu da rage yawan faduwa jarrabawa da ake samu, haka kuma zai tainakawa dorewa al’adu da hade kan al’umma.
Wakikin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewar, bayan doguwar mahawara a zauren, majalisar ta mika kudurin ya zuwa kwamitin ta na ilimi domin yi masa taza da tsifa kuma ya bawa majalisar shawarar daukar mataki na gaba.
