
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da naɗin sabbin Kwamishinoni da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya zaɓa su zama mambobin majalisar zartarwa ta jihar.
Jaridar Aminiya ta rawaito cewa, Shugaban Majalisar Rt. Hon. Jibril Ismail Falgore ne ya sanar da amincewar da sunayen da gwamna Abba Kabir Yusuf ya aika mata
Sun kuma yi hakan ne bayan tattaunawa a zamansu a ranar Talata. Inji Jaridar
A ranar Litinin ne gwamna ya aike wa da majalisar sunayen mutane shida da bukatar sahalewar majalisar na nada su kwamishinoni.

Daga baya ya sake aike ƙarin sunan Nura Iro Ma’aji, wanda majalisar ta ƙara sannan ta tabbatar da su.
Daga cikin waɗanda aka tabbatar akwai Shehu Wada Sagaji tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin, wanda aka cire daga muƙaminsa a ranar Alhamis makon jiya.
Sauran sune Abdulkadir Abdulsalam da Gaddafi Sani Shehu da Ibrahim Wayya da Dakta Dahiru Hashim Muhammad da kuma Dakta Ismail Aliyu Dan Maraya.
Ana sa rai nan gaba Gwamna Abba Kabir Yusuf zai rantsar da su da kuma ma’aikatun da za su rike.
Sabbin kwamishinonin, ana sa ran za su taimaka wajen aiwatar da manufofin gwamnan domin inganta rayuwar al’ummar Jihar Kano.