Majalisar dattijan kasar nan ta sanya ranar 17 ga watan Maris amatsayin ranar da zata kammala yin nazari da amincewa da kasafin kudin 2026 da ya zarta naira tiriliyan 58.
Kwamitin kasafin kudi na majalisar ne ya bayyana haka a ranar Juma’a inda ya amince da 2 ga wata Fabrairu zuwa 13 ga watan domin yin taza da tsifa ga kasafin a gaban kwamitin.
Haka zalika ya sanya ranar 9 ga watan Fabrairu domin sauraron ra’ayin al’umma dangane da kasafin.
Shugaban kwamitin Sanata Solomon Olamilekan Adeola ya ce an amince da ranar 5 ga wantan Maris domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki a bangaren kudi na gwamnatin tarayya.
- Majalisar Wakilai Ta Bukaci Gwamnati Ta Gina Sabbin Sansanonin NYSC
- ‘Yan Majalisar Kano 2 Sun Rasu A Rana Daya
Ya ce wadanda za a tattauna dasu sun hada da ministan kudi Wale Edun da ministan kasafin kudi da tsare tsare Atiku Bagudu.
Ya kara da cewa ranar 16 zuwa 23 ga watan Fabrairu kwamitocin majalisar dattijai zasu mika rahotonin kare kasafin kudi da ma’aikatu da hukumomin gwamnati suka yi.
