
Majalisar dattawan kasar nan ta bayyana damuwa kan gazawar gwamnatin tarayya wajen cika yarjejeniyar da ta kulla da kungiyar malaman jami’o’i ASUU, inda ta bayyana lamarin a matsayin abin da ba za a amince da shi ba.
Shugaban kwamitin majalisar mai kula da manyan makarantu Sanata Aliyu Dandutse, ne ya bayyana hakan bayan zaman sirri da shugabannin ASUU.
Wannan na zuwa ne bayan da aka fara yajin aikin gargadi na mako biyu da ASUU ta shiga sakamakon matsalolin da suka dade suna tasowa tun daga shekarar 2011.
Ya ce majalisar dattawa za ta fara tattaunawa da dukkan nmasu ruwa da tsaki, ciki har da ASUU, ma’aikatar ilimi, da hukumar kula da jami’o’i ta ƙasa NUC, domin samun mafita ta dindindin kan matsalar.
Kwamitin ya kuma shawarci ASUU da ta gabatar da cikakken jerin buƙatunta a rubuce, domin baiwa majalisar damar tantance na gaggawa da na dogon lokaci da za su taimaka wajen magance matsalolin da ke addabar fannin ilimi.
Shugaban ƙungiyar ASUU, Chris Piwuna, wanda ya yi magana a madadin ƙungiyar, ya bayyana cewa yajin aikin gargadi na mako biyu da suke yi yanzu ya samo asali ne daga matsalolin da suka dade suna faruwa tun daga shekarar 2011.