Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da karatu na biyu kan kudirin da ke neman kafa doka da manufofi don sauya tsarin sufuri daga amfani da motoci masu man fetur zuwa na lantarki.
Wanda ya dauki nauyin kudirin, Sanata Orji Uzor Kalu, ya ce manufar dokar ita ce rage hayakin da ke gurbata muhalli, karfafa masana’antar kera motoci a cikin gida, tare da bai wa Najeriya damar shiga cikin sabuwar kasuwar fasahar sufuri mai tsafta da duniya ke komawa gare ta.
A cewarsa, sashin sufuri yana da alhakin kashi 20 zuwa 30 cikin 100 na hayakin da ke haifar da dumamar yanayi a Najeriya.
Ya gargadi cewa idan ba a ɗauki mataki ba, ƙasar na iya barin sauran ƙasashen Afirka su gabace ta a fannin sabbin fasahohin sufuri.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana kudirin a matsayin “abu mai kyau,” yana mai fatan ganin yadda za a aiwatar da shi nan gaba.
Majalisar ta tura kudirin zuwa Kwamitin Majalisar kan Masana’antu, wanda ake sa ran zai gabatar da rahotonsa cikin makonni hudu.
