
Majalisar Dattawan ta umarci kwamitinta na sadarwa da ya binciki dalilan tashin farashin data tare da nemo hanyoyin rage wa al’umma sauki.
A zaman da majalisar ta gudanar a ranar Laraba, shugabanta Sanata Godswill Akpabio ya ce, ƙarin farashin na hana mutane da yawa, musamman matasa, damar amfani da Intanet.
Shugaban ya kuma jaddada cewa, samun Intanet mai araha zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da tallafa wa ƙananan ’yan kasuwa.
Majalisar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta tsara manufofi da za su tabbatar da farashi mai sauƙi.
Ta kuma bada shawarar kafa cibiyoyin fasaha masu rangwame domin amfanin ɗalibai, ’yan kasuwa, da masu aiki da fasahar zamani.
Majalisar ta bukaci Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC) da ta yi aiki tare da kamfanonin sadarwa domin rage farashin data.