Kwamitin haɗin gwiwa na Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai kan sake duba kundin tsarin mulkin kasa ya amince da ƙirƙirar sababbin jihohi guda shida a ƙasar nan.
Wannan na daga cikin muhimman matakan da aka cimma a ƙarshen taron kwana biyu da aka gudanar a Legas, ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, da Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Benjamin Kalu.
Kwamitin ya yi nazari kan kudirori 69, buƙatun ƙirƙirar jihohi 55, da kuma buƙatun ƙirƙirar kananan hukumomi 278, tare da gyaran iyakoki guda biyu.
A yayin da ake nazari kan buƙatun ƙirƙirar jihohi a jiya Asabar, mambobin kwamitin sun amince da ƙirƙirar jihohi shida wato jaha ɗaya daga kowace yankin siyasa guda shida na ƙasar.
Da wannan mataki, adadin jihohin Najeriya zai ƙaru daga 36 zuwa 42 idan majalisun biyu suka amince da rahoton.
