
Hukuncin ya biyo bayan amincewa da rahoton Kwamitin Ladabtarwa da Da’a na Majalisar wanda ya bincike ta kan zargin karya dokokin majalisar.
Hakan ya biyo bayan tattaunawa da gabatar da rahoton kwamitin a zaman Majalisar a ranar Alhamis.
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta ki bayyana a gaban kwamitin a ranar Laraba, duk da gayyatar da aka yi mata domin ta kare kanta a sakamakon haka, majalisar ta yanke hukuncin dakatar da ita har na tsawon watanni shida.
’Yar majalisar ta shiga takun saka da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, kan rabon kujeru a zauren majalisar.
Haka kuma, Natasha ta zargi Akpabio da cin mutuncinta a bainar jama’a da kuma hana ta gabatar da kudirorinta a zauren majalisar.
Kin amincewarta da sabon tsarin rabon wurin zaman ya sa Shugaban Majalisar ya hana ta damar yin magana a zauren, wanda hakan ya haifar da sabani a tsakaninsu.
Aminiya ta rawaito cewa, a sakamakon haka majalisar ta tura batun zuwa Kwamitinta na Ladabtarwa da Ɗa’a don gudanar da bincike.
A zaman kwamitin na ranar Laraba, Shugaban Kwamitin, Sanata Neda Imasuen (PDP, Edo ta Kudu), ya nuna takaicinsa kan rashin halartar Natasha.
Ya ce: “Sanata Natasha an gayyace ta zuwa wannan taro. Muna fatan za ta zo yayin da muke ci gaba da zama.”
Rashin halartar ya sanya majalisar yanke hukuncin dakatar da ita na tsawon watanni shida masu zuwa.