Majalisar Dokokin Tarayya ta amince da buƙatar Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu na neman ciyo bashi a cikin gida na naira tiriliyan 1.15, domin cike giɓin kasafin kuɗin shekara ta 2025.
A makonni biyu da suka gabata ne Shugaban Ƙasa ya aika da buƙatar zuwa majalisar, inda ya bayyana cewa ƙarin da aka samu a giɓin kasafin kuɗin, daga naira tiriliyan 12.95 zuwa naira tiriliyan 14.10 da majalisar dokokin ta amince da shi.
Kasafin kuɗin shekarar 2025 dai ya kai naira tiriliyan 59.99, kuma ana sa ran za a rufe giɓin kuɗin ta hanyar bashin cikin gida da na wajen ƙasa.
A makon da ya gabata, Najeriya ta samu kuɗaɗe har dala biliyan 2.35 ta hanyar sayen takardun lamuni.
