Hukumar ‘yan sanda a jihar Borno ta tabbatar da mutuwar mutane huɗu tare da jikkatar wasu goma bayan da wata mota ta taka bam da ake zargin ‘yan Boko Haram ne suka dasa a hanyar Damboa zuwa Maiduguri.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar, ASP Kenneth Daso, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a kauyen Komala da ke ƙaramar hukumar Konduga, lokacin da wata motar Isuzu pickup mai ɗauke da fasinjoji daga Damboa ta taka na’urar fashewa da aka binne a ƙasa.
An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Kwararru na Maiduguri domin samun kulawar gaggawa.
Wannan hari na zuwa ne mako guda bayan wani dan kunar bakin wake da ake kyautata zaton dan Boko Haram ne ya tayar da bam a kasuwar kifi da ke Konduga, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 16 tare da jikkata wasu da dama.
