Kimanin mabiya darikar Tijjaniyya miliyan uku daga ciki da wajen Najeriya ne suka hallarci bikin Mauludin Sheikh Ibrahim Nyass na shekarar 2026.
An gudanar da taron ne a Filin Wasan Muhammad Dikko da ke Katsina, inda baki daga jihohi 36, Abuja da wasu ƙasashen Afirka suka halarta.
- Samarin Tijjaniyya sun gudanar da taron zaman lafiya a Kano
- Taron mauludi ba gudu da ja da baya – Gwamnatin Kano
Malaman addini da suka hada da Sarkin Kano, Alhaji Muhammad Sanusi II, sun yi kira ga Musulmi da su bi umarnin Allah, su nemi ilimi da zaman dogaro da kai.
Gwamnan Katsina, Dikko Radda, ya gode wa masu shirya taron tare da rokon a ci gaba da addu’o’in zaman lafiya da ci gaban jihar da Najeriya baki ɗaya.
