Ma’aikatar Albarkatun Ma’adinai ta musanta zargin da Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta yi na cewa gwamnatin tarayya ta kafa masana’antar sarrafa gwal a jihar Legas, lamarin da ƙungiyar ta ce ya saɓa wa ƙa’idar daidaiton tarayya.
A wata sanarwa da Mataimaki na Musamman kan Yaɗa Labarai ga Ministan Albarkatun Ma’adinai, Dele Alake Segun Tomori, ya fitar, an bayyana cewa masana’antar da ake magana a kai ba ta gwamnati ba ce.
Wannan masana’anta aiki ne na kamfanin Kian Smith, wani kamfani mai zaman kansa.
Tikiti ya ƙara da cewa babu inda ministan ya bayyana cewa gwamnati ce ta mallaki ko ta kafa masana’antar sarrafa gwal a Legas.
A cewar Tomori, dukkan masana’antun gwal da ake shirin ƙaddamarwa a sassan ƙasar nan mallakar kamfanoni masu zaman kansu ne.
Tomori ya soki Kungiyar Dattawan Arewa bisa abin da ya kira rashin yin cikakken bincike kafin fitar da irin wannan zargi, yana mai cewa ba zai yiwu a tilasta wa kamfani mai zaman kansa ya kafa masana’antarsa a wani yanki na musamman ba.
